Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Hizbullah ta ce ta yi amfani da wani jirgin mara matuki wajen kaiwa wata motar sojoji da ke dauke da tawagar rundunar sahayoniya a garin Al-Tiba da ke kudancin Lebanon. A ciki gaba da bayar da kariya ga Lebanon da al'ummarta, a matsayin martani ga ta'addancin da gwamnatin Sahayoniya ta yi a kauyukan kudancin Lebanon da kuma mayar da martani ga karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
Kafofin yada labaran Isra'ila sun ba da rahoton cewa, wani makami mai linzami na kungiyar Hizbullah ya afkawa wani gini a garin Al-Mutlala da ke Al-Jalil al-Ali da ke arewacin Falasdinu. Rundunar sojin Isra'ila ta sanar da cewa, an harba makamai masu linzami guda hudu daga Lebanon zuwa yankin Al-jalil da ke arewacin Falasdinu. Sannan Hizbullah ta kai hari kan sansanin sojojin Isra'ila a Kiraat Shamoni da wasu jirage marasa matuka. Sannan majiyoyin Isra'ila sun ce wani makami mai linzami ya faɗa a wani gini a garin Muɗla da ke Jalil Aala a arewacin Falasdinu da aka mamaye sannan sojojin Isra'ila sun ce an harbo makamai huɗu daga Lebanon zuwa yankin Al-jalil Ulya.
Hizbullah ta sanar da cewa, mayakan gwagwarmayar Musulunci sun kai wa hedikwatar bataliyar "Al-Sahl" hari a cikin sansanin Baituhlali da makama mai linzami. Hizbullah ta fada a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, mayakan gwagwarmayar Islama sun hari taron sojojin Isra'ila a garin da ke kan iyakar Al-Quzh da manyan bindigu. Hezbollah ta kasar Lebanon ita ma a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce ta kai hari kan sansanin Philo na gwamnatin Sahayoniya a kudu da "Rabash Bina" da makamai masu linzami. Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da cewa, a mayar da martani ga mamayar da gwamnatin Sahayoniya ta yi a kauyuka da ke kudancin Lebanon, mayakan gwagwarmayar Musulunci sun harba rokoki a garuruwan Sahayoniya na Kariat Shamuneh, Marghliot, Avium da Yerun.
Bayan harin makami mai linzami na kungiyar Hizbullah, an ji karar gargadin ƙararrawa a garin Katserin da ke Golan da aka mamaye. Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da cewa, a yau ta kai hari kan wurin sojin Al-Mutlala da wani mummunan hari mai linzami. Kafofin yada labaran gwamnatin sahyoniyawan sun ba da rahoton cewa, wani makami mai linzami na Hizbullah ya afkawa garin Karmil na Sahayoniya. Kafofin yada labarai sun kara da cewa kungiyar Hizbullah ta harba makamai masu linzami guda hudu kan Karmil. Wani jirgin sama mara matuki na Hizbullah ya kai hari kan sansanin horas da Isra'iliyawa. Tashar ta 12 ta gwamnatin Sahayoniyya ta ba da rahoton cewa, wani makamai mai linzami da aka harba daga Lebanon ya haifar da mummunar illa ga muhalli a garin Naharia.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce sojoji takwas ne suka jikkata a wani harin da kungiyar Hizbullah ta kai.
Ci gaban filin daga a arewacin yankunan da aka mamaye ya shiga wani sabon mataki, kuma hare-haren makami mai linzami da jiragen sama na Hizbullah a lokaci guda sun yi matukar kawo cikas ga yanayin tsaro a wadannan yankuna. Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta fada a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce ta kai hari kan sansanin Sharagha da ke arewacin Akka, wanda aka fi sani da hedkwatar sashin Golani. Hizbullah: tayi ruwan makamai masu linzami a wuraren taruwar sojojin Isra'ila da motocinsu a Tal Shamran da kewayen Bint Jbeil.
Your Comment